Aƙalla mutane takwas sun rasa rayukansu, yayin da 18 suka jikkata, sakamakon wani mummunan fashewar bam a cikin wani masallaci a birnin Homs na ƙasar Siriya, a lokacin da ake gudanar da sallar Juma’a, in ji ma’aikatar lafiya ta ƙasar.
Rahotannin kafafen yaɗa labaran gwamnati sun nuna cewa an dasa bam a cikin Masallacin Imam Ali ibn Abi Talib, wanda ke unguwar Wadi al-Dhahab, yankin da yawancin mazauna cikinsa mabiya ƙungiyar Alawiyya ne. Hotunan da aka fitar sun nuna barnar da ta haɗa da bangon da ya ƙone, tagogi da suka tarwatse, da jini a shimfiɗar masallacin.
Mahukunta sun ce ƙungiyar masu tsattsauran ra’ayi ta Saraya Ansar al-Sunnah ta ɗauki alhakin kai harin, tana mai cewa ta yi hakan tare da wata ƙungiya da ba a bayyana sunanta ba. Ma’aikatar Harkokin Wajen Siriya ta yi Allah-wadai da harin, tana kiran sa da ta’addanci mai nufin lalata tsaro da zaman lafiyar ƙasar, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar tashin hankalin addini bayan kifar da tsohon shugaban ƙasa Bashar al-Assad.














