Shugaban Amurka Donald Trump ya ce tattaunawar da ake yi da Iran ‘mai tsari ce kuma mai amfani’ ce, kuma ya yi alƙawarin cewa takunkumi zai ci gaba har sai an kai ga yarjejeniya ta ƙarshe.
‘Takunkumin zai ci gaba da kasancewa cikakke kuma yana aiki har sai an cim ma yarjejeniya, an tabbatar da ita, kuma an sanya hannu. Dukkan ɓangarorin su ɗauki lokaci su tabbatar da cewa komai ya yi daidai. Ba za a iya yin kuskure ba!’ in ji Trump a wani rubutu a dandalinsa na Truth Social a ranar Lahadi.
Ya kuma ce dangantakar Amurka da Iran na ƙara zama ‘ta ƙwararru sosai kuma mai amfani,’ tare da gargaɗin cewa bai kamata Tehran ta ƙirƙiro ko ta mallaki makamin nukiliya ba.
Trump ya sake gode wa ƙasashen Gabas ta Tsakiya saboda ‘goyon baya da haɗin kai,’ yana cewa hulɗa za ta ƙarfafa ta hanyar karin shiga cikin Yarjejeniyar Abraham, sannan ya nuna yiyuwar cewa wata rana Iran na iya shiga wannan tsarin.
Ya soki yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015, yana kiran ta “ɗaya daga cikin mafi munin yarjejeniyoyin da aka taba yi,“ kuma ya sake zargin gwamnatin tsohon Shugaba Barack Obama da cewa yarjejeniyar ta gaza kuma ta buɗe hanya zuwa ga samar da makaman nukiliya.
Yarjejeniyar ‘Mai kyau kuma ta dace’
Trump ya ce tattaunawar yanzu da ake yi da Iran ‘ta fi kyau sosai’ kuma tana daga cikin wata hanya mafi tasiri, yana jaddada cewa wannan tsarin da ake ciki zai hana Tehran samun makaman nukiliya.
A wani rubutu na baya a Truth Social ranar Lahadi, Trump ya rubuta cewa kowace yarjejeniya da za a iya samu da Iran za ta kasance ‘mai kyau kuma ta dace,’ ba kamar yarjejeniyar nukiliyar 2015 da aka cim ma a zamanin tsohon Shugaba Barack Obama ba, wacce a cewarsa ta ba Tehran “maƙudan kuɗaɗe” da ‘babbar buɗaɗɗiyar damar samun makamin nukiliya.’
Ya ce tattaunawar da ke yi yanzu ‘saɓanin waccan ce,’ tare da bayyana cewa har yanzu ba a kammala yin sulhu kan yarjejeniyar ba.
Trump ya yi watsi da masu suka tattaunawar, yana cewa ba su ‘san komai game da’ tsarin ba, sannan ya ƙara da cewa, ba kamar gwamnatocin da suka gabata ba, shi baya ‘yin mummunar yarjejeniya.’
A halin da ake ciki, kafafen yaaɗ labarai na Iran sun ruwaito a ranar Lahadi cewa, akwai saɓanin da ba a warware ba tsakanin Iran da Amurka game da wasu tanade-tanaden yarjejeniya da za a iya samun daidaiti a kai.
‘Duk da wasu tattaunawa da aka yi a yau, yadda Amurka ta ƙi amincewa da wasu tanade-tanaden yajejeniyar, ciki har da batun sakin kadarorin Iran da aka hana ta taɓawa, har yanzu na ci gaba,’ in ji kamfanin dillancin labarai na Tasnim mai alaƙa da gwamanti.















