Nijeriya

Tinubu: Nijeriya Ta Nemi Taimakon Turkiyya domin Magance Matsalar Tsaro

Shugaba Tinubu ya ce Nijeriya ta nemi taimakon Turkiyya kan tsaro saboda jinkiri da tsadar makaman soji, tare da jaddada shirin kafa ‘yansandan jihohi.

Newstimehub

Newstimehub

27 Dec, 2025

2025 12 22t170153z 1445223891 rc2gegaabc17 rtrmadp 3 usa military africa e1766868971822

A ƙoƙarinsa na magance matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara a Nijeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta nemi taimakon ƙasar Turkiyya, sakamakon wahalar samun kayan yaƙi daga wasu ƙasashe.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne yayin karɓar baƙuncin shugabannin Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), da suka kai masa ziyarar Kirsimeti a birnin Legas.

A cewar wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa, Tinubu ya ce tsadar makaman soji da jinkirin isowarsu na kawo tsaiko ga yunƙurin gwamnati na shawo kan matsalolin tsaro, lamarin da ke sa wasu su riƙa kallon ƙoƙarin gwamnatinsa a matsayin mai rauni.

Ya bayyana cewa jiragen helikwafta huɗu da aka sayo daga Amurka ba za su iso cikin gaggawa ba, wanda hakan ya tilasta wa Nijeriya neman taimako daga Turkiyya domin ƙara ƙarfafa rundunonin tsaro.

Shugaban ya jaddada cewa gwamnati ba ta sassauta ƙoƙarinta ba duk da dabarun yaƙin ɓoye da ‘yan bindiga ke amfani da su, yana mai cewa ana ci gaba da ɗaukar matakai domin dawo da zaman lafiya a ƙasar.

Haka kuma, Tinubu ya sake jaddada aniyarsa ta aiwatar da tsarin ‘yansandan jihohi, yana mai cewa da zarar majalisun dokoki sun kammala gyare-gyaren doka da ake buƙata, za a fara aiwatar da tsarin tsaron na jihohi da al’umma.