Nijeriya Tsaro

Hukumar Shige da Fice Ta Kubutar da Mutane 22 Daga Hannun Masu Safarar Mutane a Katsina

Wannan aiki ya sake nuna kudirin Hukumar Shige da Fice na murkushe masu safarar mutane da kare matasa daga fadawa tarkon tafiya ba bisa ka’ida ba.

Newstimehub

Newstimehub

26 Jan, 2026

e42121e691139643fe9af647bd12c3364171d55edac989c52400b439671f04e8

A wani samame da jami’an Hukumar Shige da Fice ta ƙasa suka gudanar a Zango, jihar Katsina, an kubutar da mutum 22 da ake zargin ana ƙoƙarin safarar su.

Wannan nasara ta samu ne sakamakon rahotannin sirri daga wasu mazauna yankin, waɗanda suka lura da motsin wasu mutane da ake zargi a wani gida da bai gama ginawa ba da ke ƙauyen Maibara.

Kwamandan iyakar Jibia, Haruna Zakirai, ya ce an kai samamen ne tare da hadin gwiwar ‘yan sandan Daura, inda aka ceto mata 11 da maza 11 masu shekaru 17 zuwa 35 daga jihohi daban-daban, ciki har da Legas, Rivers, Imo, Benue da Abuja.

Bincike ya nuna ana shirin kai su Libya ne ta hanyoyin da ba bisa ka’ida ba, daga nan kuma a wuce da su Turai da sunan neman rayuwa mai kyau. Daya daga cikin wadanda aka ceto dan kasar Togo ne, yayin da babban jagoran masu safarar, wanda ake kira “Cargo”, ya tsere kuma ana nemansa.

 

Majiyar Labari: TRT HAUSA