Nijeriya

Shugaba Tinubu Ya Nufi Turai Don Ci Gaba da Hutun Karshen Shekara, Zai Kuma Ziyarci UAE

Shugaba Tinubu ya tafi Turai domin hutun karshen shekara, sannan daga nan zai ziyarci Abu Dhabi don halartar taron duniya kan cigaba mai ɗorewa, kafin ya koma Najeriya.

Newstimehub

Newstimehub

28 Dec, 2025

452124243e01d1dd6270b58dedb75444a3e6a11c4ba304f82795f6cfad7ae110 e1767033108724

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya baro Lagos zuwa Turai domin ci gaba da hutun karshen shekararsa, kamar yadda fadar shugaban kasa ta tabbatar. Wannan tafiyar kuma ta zo ne a daidai lokacin da ake sa ran zai yi wasu muhimman harkoki na diflomasiyya kafin komawarsa gida.

Shugaban ya tashi ne ranar Lahadi zuwa Turai, sai dai sanarwar mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, bai bayyana takamaiman kasar da zai sauka ko tsawon lokacin da zai yi a can ba.

Duk da haka, an tabbatar da cewa daga Turai zai zarce Abu Dhabi a Hadaddiyar Daular Larabawa bisa gayyatar Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan domin halartar taron mako guda na Abu Dhabi Sustainability Week 2026 (ADSW 2026) da za a gudanar a farkon watan Janairu.

Wannan taro na haɗa shugabannin duniya, ‘yan kasuwa da manyan masu ruwa da tsaki domin tattauna dabarun cigaba mai ɗorewa. Bayan kammala taron ne ake sa ran Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya.

A baya dai, a watan Satumba, shugaban ya yi kusan kwana 10 a Faransa da Birtaniya a wani ɓangare na hutun shekararsa.

Majiyar Labari: Trt Hausa