Ina jin takaici matuƙa ganin yadda rikicin Sudan ke ƙara tsananta, abin da ya tilasta dubban mutane barin gidajensu domin neman tsira. Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) ta bayyana cewa sama da fararen-hula 4,000 ne suka tsere daga yankunan Kordofan a cikin kwanaki uku sakamakon matsalar tsaro da ke ƙara muni. Rahoton ya ce tsakanin 1,500 zuwa 2,500 sun gudu daga Al-Kuweik na Kudancin Kordofan, tare da ƙarin mutane 375 daga Kadugli da 495 daga Dilling tsakanin 27 zuwa 29 ga Disamba.
IOM ta bayyana cewa waɗannan ’yan gudun hijirar sun tsinci kansu a wurare daban-daban a Arewacin Kordofan, Kudancin Kordofan da White Nile. A Arewacin Kordofan kaɗai, an samu rahoton mutane 1,020 da suka bar kauyukan Um Taghirat da Al-Markha saboda ƙarin tabarbarewar tsaro, inda da dama suka nufi Omdurman a yammacin Khartoum. A baya kuma hukumar ta tabbatar da cewa mutane 1,290 sun rasa matsuguni saboda wannan rikici.
Jihohin Kordofan uku – Arewa, Yamma da Kudu – na fama da faɗa mai tsanani tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF, wanda ya tilasta dubban mutane barin yankunansu. Yanzu haka RSF na da ikon yawancin jihohin Darfur, yayin da sojojin Sudan ke riƙe da mafi yawan sauran jihohi da suka rage ciki har da babban birnin Khartoum. Wannan rikici, wanda ya fara tun Afrilu 2023, ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da matsugunansu.














