Sabon tashin hankali ya sake kunno kai a gabashin Jamhuriyar Dimokiradiyyar Kongo yayin da aka samu gagarumin fada tsakanin sojojin gwamnati da ƙungiyar ‘yan tawayen M23 a yankunan da ke kewaye da birnin Uvira, wani muhimmin gari a lardin Kivu ta Kudu.
Rahotanni sun ce rikicin ya ɓarke tun da safiyar Asabar a garuruwa da dama da ke kusan kilomita 10 daga Uvira, inda aka ji harbe-harbe da fashe-fashe a wuraren Kashombe, Lubanda, Musingwe, Katongo da Kigongo.
Wannan sabon rikici ya faru ne duk da yarjejeniyar sulhu da DRC da Rwanda suka rattaba hannu a Washington karkashin shiga tsakani na Donald Trump. Duk da cewa M23 ta sanar a baya cewa za ta janye daga Uvira, rikicin ya sake tashi kuma rahotanni sun nuna cewa mata da yara sun ji rauni a wasu hare-haren da suka kai ga mutuwa da jikkatar fararen hula.
A yankin Kivu ta Arewa ma, an ruwaito mutane akalla shida sun mutu yayin da wasu fiye da 40 suka ji rauni bayan harin da aka danganta wa rundunar sojin Kongo.














