Shugaban Amurka Donald Trump ya sake ɗaga sautin barazana kan rikicin Venezuela, yana mai gargaɗin sabuwar shugabar rikon ƙwarya ta ƙasar cewa dole ta yi biyayya ga bukatun Washington ko kuma ta fuskanci mummunan sakamako.
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa shugabar rikon ƙwarya ta Venezuela, Delcy Rodriguez, za ta “biya babban farashi” idan ba ta yi abin da Amurka ke so ba, bayan cafke tsohon shugaban ƙasar Nicolas Maduro da sojojin Amurka suka yi.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da mujallar The Atlantic, Trump ya ce idan Rodriguez ba ta yi aiki da muradun Amurka ba, sakamakon da za ta fuskanta zai fi wanda Maduro ya fuskanta tsanani. Wannan barazana ta zo ne a daidai lokacin da Kotun Ƙoli da sojojin Venezuela suka tabbatar da Rodriguez a matsayin shugabar rikon ƙwarya.
A ranar Asabar, sojojin Amurka sun kai hari Caracas da asubahin safiya, inda suka lalata wasu wuraren soji tare da kwashe Maduro da matarsa zuwa New York domin fuskantar tuhume-tuhumen safarar miyagun ƙwayoyi. Gwamnatin Trump ta ce a shirye take ta yi aiki da sauran sassan gwamnatin Venezuela muddin bukatunta sun cika, ciki har da buɗe ƙofofi ga jarin Amurka a fannin man fetur na ƙasar.
Rodriguez ta nuna rashin tsoro bayan harin, tana mai cewa Maduro ne halastaccen shugaban ƙasar, tare da jaddada aniyar kare albarkatun ƙasa. Sai dai Trump ya ce Amurka za ta iya “tafiyar da” Venezuela, yana mai kare ra’ayin sauya gwamnati da sake gina ƙasar, wanda ya bayyana a matsayin mafi alheri fiye da halin da take ciki a yanzu.
Baya ga Venezuela, Trump ya kuma maimaita bukatarsa ta ganin Greenland, wacce ke ƙarƙashin Denmark, ta shiga cikin Amurka, yana mai cewa ƙasar na da muhimmanci ga tsaron Amurka.














