Tarayyar Turai na shirin kai wata ziyara ta tarihi zuwa Damascus, bayan faduwar mulkin Bashar al-Assad a ƙarshen shekarar 2024. Shugaban Majalisar Tarayyar Turai, European Council Antonio Costa, da shugabar Hukumar Tarayyar Turai, European Commission Ursula von der Leyen, za su isa babban birnin Syria a ranar Juma’a, a cewar majiyoyin gwamnati.
Ziyarar ita ce ta farko da manyan shugabannin Tarayyar Turai za su kai Damascus tun bayan sauyin mulki, kuma za su gana da shugaban Syria Ahmad al-Charaa. Wannan mataki na nuna sabon salo a dangantaka tsakanin Tarayyar Turai da sabbin hukumomin Syria.
A cewar Majalisar Tarayyar Turai, ziyarar na cikin wata rangadi ta Gabas ta Tsakiya da ta haɗa da Jordan da Lebanon, inda shugabannin EU za su tattauna batutuwan tsaro, siyasa da tallafin jin kai. EU ta bayyana aniyarta ta tallafa wa zaman sauyi, kwanciyar hankali da sake gina Syria.
Tun farkon 2025, Tarayyar Turai ta fara sassauta matsayinta kan Damascus, inda ta cire takunkuman tattalin arziki da aka kakabawa ƙasar a zamanin tsohon mulki. Ziyarar na daga cikin ƙoƙarin EU na goyon bayan tsarin siyasa da Syrians kansu ke jagoranta tare da kiyaye ‘yancin kai da cikakken ikon ƙasar.














