Ma’aikatar Tsaron Syria ta sanar da tsagaita wuta a unguwannin Ashrafieh, Sheikh Maqsoud da Bani Zeid na arewacin Aleppo, inda ta ce matakin ya fara aiki da misalin ƙarfe 3:00 na asuba ranar Juma’a.
Hukumomi sun bayyana cewa an bai wa ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai wa’adin ficewa daga yankunan kafin ƙarfe 9:00 na safe domin kawo ƙarshen yanayin soja.
Sanarwar ta biyo bayan shigar jami’an tsaron cikin gida bayan ficewar PKK/YPG daga wasu yankuna, tare da kai hare-hare kan wuraren YPG sakamakon zargin kashe fararen hula tara.
Gwamnati ta ce YPG ba ta aiwatar da yarjejeniyar da aka rattaba hannu a kanta a watan Maris 2025 ba, yayin da take ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar bayan kifar da mulkin Bashar al-Assad.













