Turkiyya ta bayyana cewa tana sanya ido sosai kan halin da ake ciki a Siriya, tana mai jaddada muhimmancin haɗin kan siyasar ƙasar, tsaron iyakoki da tsarin gwamnati. Majiyoyin tsaron Turkiyya sun shaida wa TRT World cewa Ankara na ɗaukar rikicin a matsayin barazana kai tsaye ga tsaron ƙasarta.
Hukumar leƙen asiri ta ƙasa (MIT) na mai da hankali kan rage tasirin rikicin kan iyakar Turkiyya, tare da bibiyar yiwuwar kwararar ’yan gudun hijira da kare fararen hula. An ce an fi mayar da hankali kan sabon tashin hankalin da ya barke a Aleppo, musamman a unguwannin Sheikh Maqsoud, Ashrafiyeh da Beni Zaid, inda ake fafatawa tsakanin sojojin Siriya da ’yan YPG.
Majiyoyin sun ce rikicin ya sake barkewa ne bayan YPG ta karya yarjejeniyar da aka cimma da gwamnatin Siriya a ranar 10 ga Maris. An zargi ƙungiyar da haddasa mutuwar fararen hula akalla takwas tare da tilasta wa dubban mutane barin muhallansu.
Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojin Siriya ta karɓe iko da Ashrafiyeh da Beni Zaid, yayin da aka ayyana tsagaita wuta domin bai wa YPG damar janyewa zuwa gabashin Kogin Furat. Amurka da Turkiyya sun yaba da wannan mataki, suna cewa zai taimaka wajen hana ƙarin zubar da jini.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan na bibiyar lamuran kai tsaye, yayin da MIT ke ci gaba da tuntuɓar Amurka da Siriya. Ankara ta ce burinta shi ne zaman lafiya mai ɗorewa a Siriya, tare da kiyaye cikakken ikon ƙasar da tsaron iyakokinta.














