Wutar daji mai tsanani na ci gaba da addabar jihar Victoria a kudu maso gabashin Australia, inda aka lalata akalla gine-gine 130, lamarin da ya sa mahukunta suka ayyana halin bala’i domin kare rayuka da dukiyoyi.
Rahotanni sun ce gobarar, wadda ta zarce 35, ta tilasta ficewar al’umma daga yankuna da dama yayin da wutar ke kara yaduwa ba tare da cikakken iko ba. Hukumomi sun ce kusan gidaje 20,000 sun rasa wutar lantarki, musamman a yankunan karkara.
Gobarar ta cinye kimanin hekta 300,000 na filaye zuwa yanzu, yayin da aka kakabawa jihar Victoria dokar hana kunna wuta gaba ɗaya.
A wani bangaren kuma, an samu bullar wani guguwar iska mai karfin mataki na biyu a gabar arewacin Queensland, wadda ake fargabar za ta haddasa ambaliyar ruwa da lalata gidaje.
Hukumomi sun gargadi jama’a da su kiyaye matakan tsaro, musamman duba da tsananin zafin rana da Australia ta Kudu ke fuskanta, wanda ke daga cikin mafi muni a tarihin kasar.









