Majalisar dokokin New South Wales a Australia na ci gaba da gudanar da muhawara kan sauye-sauyen dokoki da ake shirin gabatarwa dangane da mallakar bindiga, biyo bayan kisan mutane da dama da aka yi a wani wajen bikin addinin Yahudawa a bakin teku na Bondi a makon da ya gabata.
Harin ya yi sanadin mutuwar mutane 15. Ƙudurin da ake sa ran zai samu amincewa ya ƙunshi taƙaita adadin bindigogin da mutum ɗaya zai iya mallaka a jihar. Sai dai ƙungiyar masu rajin bayar da ’yancin mallakar bindiga ta nuna damuwa, tana mai cewa ana gaggauta aiwatar da ƙudurin, kuma hakan zai shafi masu bin doka da suka mallaki bindiga bisa ƙa’ida.
A matakin tarayya kuma, Firaministan Australia, Anthony Albanese, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta nemi samar da sababbin dokoki domin yaƙi da tsattsauran ra’ayi da kalaman kiyayya a faɗin ƙasar.









