Yanayin tsaro ya ƙara tabarɓarewa a birnin Kadugli da ke Kudancin Kordofan, lamarin da ya tilasta daruruwan mutane tserewa domin tsira da rayukansu. Hukumar Kula da Masu Ƙaura ta Duniya (IOM) ta bayyana cewa aƙalla mutum 570 ne suka rasa matsugunansu tsakanin ranakun 8 zuwa 10 ga watan Janairu, bayan sabbin hare-hare sun ƙara ƙamari a yankin.
Hukumar ta ce halin da ake ciki a Kadugli na cike da “rashin tabbas da hatsari,” kuma mafi yawan mutanen da suka tsere sun nufi Jihar White Nile. IOM ta ƙara da cewa tana ci gaba da sa ido kan lamarin, yayin da a baya ta ruwaito cewa adadin masu ƙaura a jihohin Kordofan uku ya haura 64,000 sakamakon rikicin da ke gudana.














