Afirka Sudan Tsaro

Sabbin Hare-hare a Kudancin Kordofan Sun Tilasta Daruruwan Jama’a Barin Gidajensu

Fiye da mutum 500 sun tsere daga birnin Kadugli a Sudan sakamakon tsanantar faɗa, inda da dama suka nufi Jihar White Nile domin neman tsira.

Newstimehub

Newstimehub

12 Jan, 2026

00ce8c4d 34e2 4f09 a696 6b5195bdfdce

Yanayin tsaro ya ƙara tabarɓarewa a birnin Kadugli da ke Kudancin Kordofan, lamarin da ya tilasta daruruwan mutane tserewa domin tsira da rayukansu. Hukumar Kula da Masu Ƙaura ta Duniya (IOM) ta bayyana cewa aƙalla mutum 570 ne suka rasa matsugunansu tsakanin ranakun 8 zuwa 10 ga watan Janairu, bayan sabbin hare-hare sun ƙara ƙamari a yankin.

Hukumar ta ce halin da ake ciki a Kadugli na cike da “rashin tabbas da hatsari,” kuma mafi yawan mutanen da suka tsere sun nufi Jihar White Nile. IOM ta ƙara da cewa tana ci gaba da sa ido kan lamarin, yayin da a baya ta ruwaito cewa adadin masu ƙaura a jihohin Kordofan uku ya haura 64,000 sakamakon rikicin da ke gudana.

Majiyar Labari: TRT HAUSA