Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta sanar da naɗa ɗan Ghana, Daniel Nii Laryea, a matsayin alkalin tsakiya na wasan semi-final na gasar AFCON 2025 da za a fafata tsakanin Nijeriya da Morocco. Za a buga wasan ne a filin Prince Moulay Abdellah da ke Rabat a daren Laraba, da ƙarfe 9:00 na dare agogon Nijeriya.
CAF ta ce Zakhele Siwela daga Afirka ta Kudu da Souru Phatsoane daga Lesotho za su kasance mataimakan alkalai, yayin da Arsénio Maringule na Mozambique zai zama alkalin taimako na uku. Samuel Uwikunda na Rwanda kuma zai kasance jami’in karshe na kula da wasan.
Nijeriya ta kai wannan mataki ne bayan ta doke Algeria da ci 2–0 a wasan kwata-final, tare da zama ƙungiyar da ta fi zura ƙwallaye a gasar, inda ta ci kwallaye 14, lamarin da ya karya tarihin da ta kafa a baya.
Wasan zai kuma sake hura wutar hamayya tsakanin ƙasashen Afirka masu ƙarfi a fannin kwallon kafa, yayin da aka dora wa alkalai nauyin tabbatar da adalci da kwanciyar hankali a wannan gagarumin karawa.














