Wata babbar tawaga daga Rundunar Sojin Amurka ta Afirka (US AFRICOM) ta sake jaddada aniyarta ta ƙarfafa haɗin gwiwa da Hukumar Yaki da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA), tana mai alkawarin ci gaba da bayar da tallafi a yaƙin da ake yi da safarar kwayoyi.
Tawagar ta kai ziyara hedikwatar NDLEA da ke Abuja a ranar Talata, 13 ga Janairu 2026, inda ta gana da Shugaban Hukumar, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya). A yayin ganawar, jami’an sun yaba da kyakkyawar alaƙar aiki tsakanin NDLEA da hukumomin tsaro na Amurka.
Shugaban tawagar, Philip Esch na Hukumar DEA, ya bayyana haɗin gwiwar a matsayin “muhimmi kuma mai daraja” ga gwamnatin Amurka, yayin da James Elseth ya ce ayyukan NDLEA na taka rawa wajen ƙarfafa tsaron yankin da na duniya. Ya ƙara da cewa ana aiwatar da manyan shirye-shiryen tallafi guda biyu, tare da horaswa ga jami’an NDLEA.
A nasa jawabin, Marwa ya nuna godiya ga AFRICOM da gwamnatin Amurka, yana mai jaddada cewa haɗin gwiwar ƙasashen waje na da matuƙar muhimmanci wajen yakar fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma alaƙarsa da ta’addanci. Ya kuma bukaci ƙarin tallafi a bangarorin kayan binciken dijital, na’urorin gano kwayoyi, na’urorin duba kaya a filayen jiragen sama, dakunan gwaje-gwaje da karnukan bincike.














