Nijeriya Tsaro

Sojojin Operation Hadin Kai Sun Dakile Manyan Hare-hare, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda a Borno da Adamawa

Sojojin Nijeriya sun samu gagarumar nasara bayan sun hallaka ’yan ta’adda da dama tare da dakile hare-hare a Borno da Adamawa ba tare da asarar rai a bangarensu ba.

Newstimehub

Newstimehub

17 Jan, 2026

abae4ae0d70ac11bf9c02a874652b6691144f92098b1af87f8e0d0afc89ff149

A ci gaba da ƙoƙarin da sojojin Nijeriya ke yi na kawo ƙarshen ta’addanci a Arewa maso Gabas, dakarun Operation Hadin Kai sun samu babbar nasara bayan sun dakile jerin hare-hare da ’yan ta’adda suka kai a jihohin Borno da Adamawa, inda suka hallaka da dama daga cikinsu tare da kwato muggan makamai, lamarin da ya sake tabbatar da ƙarfinsu da shirin kare rayukan fararen hula.

Sojojin sun fatattaki ’yan ta’adda da suka yi yunƙurin kwace sansanin sintiri a Madagali, Jihar Adamawa, tare da hallaka da dama daga cikinsu ba tare da asara a bangaren sojoji ba. A rana ɗaya, an kuma dakile wani babban hari da aka kai sansanin FOB Azir a Jihar Borno, inda sojoji tare da taimakon jiragen sama suka tilasta wa maharan janyewa, suka kwato makamai masu yawa ciki har da bama-bamai, harsasai da roka, tare da tabbatar da tsaron yankunan.

Majiyar Labari: TRT HAUSA