A ‘yan kwanakin nan dai dakarun tsaro na ci gaba da samun nasarori kan masu tayar da ƙayar baya a Arewa maso Gabas. Wannan karon ma, sun sake cafke wani da ake zargi da tallafa wa ‘yan ta’adda da kayayyakin aiki masu muhimmanci.
Sanarwar da jami’in watsa labarai na OPHK, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar ta ce an kama Dauda Usman Gubula mai shekara 64 a tashar mota ta Madagali, yayin da yake ƙoƙarin kai wa ‘yan Boko Haram jirage marasa matuƙa guda biyu tare da kayan gyaransu da fawabank na sola guda 20.
Haka kuma, dakarun sun kashe wani kwamandan ‘yan ta’adda mai suna Abdullahi Mafa a wani kwanton-ɓauna kusa da kogin Visik. An same shi da bindiga ƙirar AK47 da ƙwanson harsasai masu cike.
A wani samame dabam, an kama Ismail Muhammed mai shekara 28 a yankin Visik, ƙaramar hukumar Hong ta Jihar Adamawa, bisa zargin safarar kayayyaki ga ‘yan ta’adda. An ƙwace daga hannunsa ƙwanson harsasai, harsasai da wasu kayayyakin sojoji.
Bugu da ƙari, dakarun OPHK tare da ‘yan sa-kai sun daƙile yunƙurin masu tayar da ƙayar baya a Ngamdu, Jihar Borno, inda suka kashe wani da ake zargi infoma ne na ‘yan ta’adda yayin ƙoƙarin ketare shingen tsaro.
Majiyar Labari: TRT HAUSA














