A wani muhimmin yunƙuri na kawo sauyi a fannin kiwon lafiya a Afirka, Gidauniyar Bill Gates da kamfanin OpenAI sun ƙaddamar da wani babban shirin haɗin gwiwa da nufin amfani da fasahar AI domin inganta kulawar lafiya a ƙasashen da ke fama da ƙarancin ma’aikata, kayan aiki da kuma raguwar tallafin ƙasashen duniya.
Shirin mai suna Horizon1000, wanda kudinsa ya kai dala miliyan 50, zai yi aiki tare da shugabannin Afirka domin nemo hanyoyin amfani da fasahar AI wajen ƙarfafa tsarin kiwon lafiya, inda ake sa ran fara gwaji a Rwanda.
Bill Gates ya ce AI na iya taimakawa ƙasashe masu ƙarancin ma’aikatan lafiya da kayan more rayuwa, musamman bayan da tallafin jinƙai daga ƙasashen duniya ya ragu da kashi 27% a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ƙarin mace-macen yara. Ya ƙara da cewa amfani da fasahar zamani zai taimaka wajen dawo da ci gaban kiwon lafiya kan turba.














