Jami’ar Ibadan (UI) ta sake dawowa kan kololuwa a fagen ilimi a Najeriya, bayan da ta zama jami’a mafi daraja a ƙasar a cikin jerin Times Higher Education (THE) World University Rankings 2026. Wannan nasara ta tabbatar da matsayin UI a matsayin cibiyar ilimi mafi inganci a Najeriya a halin yanzu.
A cewar rahoton da aka fitar a ranar Alhamis, an sanya UI a rukunin duniya na 801–1000, lamarin da ya ba ta damar zarce manyan jami’o’i irin su Covenant University, University of Lagos (UNILAG), da University of Nigeria, Nsukka (UNN). Wannan ya nuna dawowar UI saman bayan da ta sauka zuwa matsayi na huɗu a 2025, duk da cewa ita ce ta fi kowa a 2023.
Kididdigar THE ta 2026 ta tantance jami’o’i 2,191 daga ƙasashe 115, ta amfani da ma’auni 18 da suka haɗa da koyarwa, bincike, ingancin wallafe-wallafe, haɗin gwiwar masana’antu, da alaƙar ƙasashen waje.
A Najeriya, UI da UNILAG kaɗai ne suka shiga cikin jami’o’in duniya 1000 na farko, yayin da jami’o’i 51 gaba ɗaya suka samu shiga cikin jerin.
Manyan Jami’o’in Najeriya a 2026 (THE Ranking):
University of Ibadan (UI)
University of Lagos (UNILAG)
Bayero University Kano (BUK)
Covenant University
Landmark University
Ahmadu Bello University
University of Ilorin
University of Jos
University of Nigeria, Nsukka (UNN)
Babcock University
Delta State University, Abraka
Ekiti State University
Federal University of Agriculture, Abeokuta
Federal University of Technology, Akure
Federal University of Technology, Owerri
Federal University Oye-Ekiti
Ladoke Akintola University of Technology
Lagos State University
Nnamdi Azikiwe University
Obafemi Awolowo University
University of Benin
University of Calabar
University of Port Harcourt














