Najeriya

Kotu Ta Yanke Hukunci a Bangaren Falana, Ta Ci Tarar Meta Dala $25,000 Kan Keta Sirri

Babbar Kotun Jihar Legas ta bai wa Lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana (SAN), nasara a ƙarar da ya shigar kan Meta, inda ta umarci kamfanin da biyan diyyar dala $25,000 saboda keta sirrinsa.

Newstimehub

Newstimehub

14 Jan, 2026

IMG 3297

Babbar Kotun Jihar Legas da ke Tafawa Balewa Square ta yanke hukunci a ranar Talata a bangaren fitaccen lauya, Femi Falana (SAN), tare da umartar kamfanin Meta Platforms Inc. da biyan diyyar dala $25,000 saboda keta haƙƙinsa na sirri. Falana ya shigar da ƙarar ne yana zargin Meta da wallafa wani bidiyo na ƙarya a shafinta da ke nuna kamar yana fama da cutar “Prostatitis,” wanda hakan ya sabawa tanadin sashe na 37 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.

Mai shari’a Olalekan Oresanya ya ce kamfani irin Meta, wanda ke samun riba daga tallace-tallace da rarraba bayanai, na da alhakin kula da sahihancin abin da ake wallafawa a dandalinsa. Kotun ta ƙi karɓar hujjar cewa Meta “mai masaukin bayanai kawai ce,” tana mai jaddada cewa kamfanin na da ikon tacewa, rarrabawa da kuma samun riba daga abun da ake yadawa, don haka yana da alhakin sakamakon ƙarya ko ɓarna da ke fitowa daga shafinsa.

Falana ya bayyana cewa bidiyon ƙarya ya ɓata sunansa tare da jefa shi cikin damuwar tunani da ta zuciya. Kotun ta kuma tabbatar da cewa kasancewar mutum fitaccen ɗan ƙasa ba ya tauye masa haƙƙin kare bayanan lafiyarsa, inda ta ce bayanan lafiya na da kariya ta musamman a ƙarƙashin Dokar Kare Bayanai ta Nijeriya (NDPA) ta 2023.

Lauyansa, Olumide Babalola, ya ce hukuncin ya kafa muhimmiyar ka’ida a Nijeriya, yana nuna cewa manyan kamfanonin fasaha ba za su ƙara fakewa da hujjar “mu dandali ne kawai” ba idan aka tabbatar da cewa sun yi sakaci wajen hana yaɗuwar bayanan ƙarya masu cutarwa.

Majiyar Labari: Channels News