Bayan koke-koken mazauna yankin ACO Estate a Abuja, Gwamnatin Tarayya ta rufe wani wurin hako duwatsu da kamfanin Dai Jin Jia Investment Limited ke gudanarwa. Hukumar NESREA ta ɗauki matakin ne bayan zargin cewa ana yin fashewar duwatsu ba tare da tsari ba, lamarin da ya jefa rayuka da dukiyoyin al’umma cikin haɗari.
Rahotanni sun nuna cewa ayyukan fashewar sun lalata gine-ginen mazauna yankin, har ma ana zargin sun haddasa mutuwar wani ƙaramin yaro. Hukumar ta ce kamfanin ya karya dokokin muhalli da suka tanadi yadda ya kamata a gudanar da irin waɗannan ayyuka a Nijeriya.

An kuma bayyana cewa kamfanin bai mallaki takardun izini da sahihin shirin fashewa ba kafin gudanar da ayyukansa. A yayin da jami’an NESREA suka je rufe wurin, an ce sun fuskanci turjiya daga jami’an tsaro da ke gadin wurin kafin daga bisani aka kulle shi.
Hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da sa ido domin tabbatar da cewa kamfanoni suna bin ƙa’idojin muhalli, tare da kare lafiyar jama’a da muhalli.














