Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama, ya sanar da fara sabon tsarin karin albashi ga sojoji daga watan Maris, tare da biyan bashin albashin watannin Janairu da Fabrairu, yayin taron 2025 West African Soldiers’ Social Activity (WASA) da aka gudanar a hedkwatar rundunar soji a birnin Accra.
A cewarsa, shekaru hudu bayan 2020, gwamnatin da ta gabata ba ta tanadi kudade domin sabon tsarin kudin gratuti ba, lamarin da ya jawo bashin sama da cedi biliyan daya ga kimanin sojoji 3,000 da suka yi ritaya.
Shugaba Mahama ya bayyana cewa ya umarci Ma’aikatar Kudi da ta fara biyan sojojin ritaya, musamman wadanda shekarunsu suka kai 95 zuwa 96, tare da shirin kammala biyan sauran basussuka.
Majiyar Labari: TRT HAUSA













