Gwamnatin Ghana tare da Jami’ar Ghana, kamfanin Google da Global Disability Innovation (GDI) Hub sun fara wani gagarumin shiri na ƙirƙirar fasahar gane murya da kayan aikin basirar wucin-gadi (AI) a harsunan gida kamar Twi, Ewe da Dagbani, domin sauƙaƙa samun ilimi da ayyukan intanet ga al’umma.
Ministan Ilimi, Haruna Iddrisu, ya bayyana hakan bayan ganawa da shugabannin Google a taron Generative AI Summit da aka gudanar a Birtaniya, inda ya ce ana mai da hankali musamman kan gane lafazin mutane da ke da nakasa da kuma ƙananan yaruka don bunƙasa samun ilimi da ayyukan dijital.
Iddrisu ya kuma ce Google ta amince da samar da kayan aikin ilimi kyauta ba tare da amfani da data ba, tare da buƙatar a haɗa harshen Hausa cikin shirin, domin ƙara faɗaɗa amfani da fasahar a Ghana da ma faɗin Yammacin Afirka. Shirin ya zo ne a ƙarƙashin jarin dala miliyan 37 da Google ta zuba a fannin AI a Afirka, ciki har da kafa cibiyar binciken AI ta farko a Accra.














