Jami’an Sin sun mika wata cibiyar karɓar bayanan tauraron dan adam ga Namibiya a wajen birnin Windhoek, a cewar kafafen yada labarai na Sin. Matakin na nuna ci gaba a faɗaɗa shirin sararin samaniyar Sin a ƙasashen waje, musamman a Afirka.
Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya ce cibiyar da Sin ta gina za ta ƙarfafa damar Namibiya wajen karɓa da sarrafa bayanan tauraron dan adam, musamman na na’urorin hangen nesa daga sama. Ma’aikatar Ilimi da Ƙirƙira ta Namibiya ta bayyana cibiyar a matsayin muhimmin ci gaba ga fasaha, tana mai cewa za ta taimaka wajen kula da bala’o’i, tsaron ƙasa, da ci gaba mai ɗorewa.
Jakadan Sin a Namibiya, Zhao Weiping, ya jaddada cewa Namibiya ce za ta mallaki cibiyar gaba ɗaya tare da sarrafa ta da kanta. Ya kara da cewa kwararrun Sin za su ci gaba da bayar da tallafin fasaha ga ma’aikatan cikin gida 14 da aka horas.
Haka kuma, an ce ana shirin aiwatar da mataki na biyu na cibiyar, yayin da Sin ke ci gaba da faɗaɗa haɗin gwiwar sararin samaniya a nahiyar Afirka.
Majiyar Labari: TRT AFRIKA














