Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergey Ryabkov, ya karyata ra’ayoyin da ke cewa ƙungiyar BRICS na ƙoƙarin rikidewa zuwa kawancen soja. A wata hira da TASS, ya jaddada cewa BRICS ba kawancen soja ba ne, kuma ba ta da wata yarjejeniya ta taimakon soja tsakanin mambobi.
Ryabkov ya ce ajandar BRICS ba ta ƙunshi atisayen soja ko sarrafa makamai, yana mai cewa har ila yau atisayen ruwan da aka yi a Afirka ta Kudu ba wani “taron BRICS” ba ne. Ya bayyana cewa ƙasashen da suka halarta sun yi hakan ne a matsayinsu na ƙasa-ƙasa, ba a karkashin BRICS ba.
Dangane da batun tsaro, jami’in na Rasha ya ce BRICS na iya taimakawa ne wajen inganta harkokin kasuwanci da kariya daga takunkumi, amma batutuwan tsaro na soja dole ne a warware su ta wasu hanyoyi daban. Ya kuma ce BRICS na iya nuna goyon baya ga Iran, yana mai nuni da hulɗar Moscow da Beijing da Tehran.
Ya kara da cewa cinikayya tsakanin ƙasashen BRICS na ƙaruwa fiye da matsakaicin duniya, yana mai bayyana hakan a matsayin alamar muhimmancin ƙungiyar. A gefe guda, ya yi ishara da ci gaba da tattaunawar Iran da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani.
MajiyarLabari: TRT AFRIKA














