Rundunar juyin-juya-halin Iran (IRGC) ta fara wani atisayen soji a mashigin tekun Hormuz, kwana ɗaya kafin a fara zagaye na biyu na tattaunawa a kaikaice tsakanin Iran da Amurka. Sanarwar IRGC ta ce atisayen, mai taken “Smart Control of the Strait of Hormuz,” na da nufin tantance shirye-shiryen tsaro da ƙarfin dakarun ruwan ƙasar.
Hukumar ta bayyana cewa atisayen ya mayar da hankali kan martani na gaggawa da kariya daga barazanar tsaro a yankin. Mashigin tekun Hormuz na da matuƙar muhimmanci a harkokin safarar mai da cinikayyar duniya, abin da ke sa duk wani motsi a yankin ya ja hankalin ƙasashen duniya.
Atisayen na zuwa ne yayin da ake fuskantar ƙarin ce-ce-ku-ce tsakanin Tehran da Washington, musamman bayan rahotannin jibge jiragen ruwa da na yaƙi a yankin. Wannan yanayi ya kara nuna tasirin siyasa da tsaro da mashigin ke da shi a yankin Gabas ta Tsakiya.
A baya-bayan nan, Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da shirin tura wani jirgin ruwa mai ɗauke da jiragen yaƙi zuwa yankin, lamarin da ke ƙara ɗora hankula kan yanayin tsaro a Hormuz.
Majiyar Labari: TRT HAUSA














