Gabas Ta Tsakiya

Turkiyya ta ce NATO ta dakile makami mai linzami daga Iran a Gabashin Bahar Rum

Turkiyya ta ce NATO ta dakile wani makami mai linzami daga Iran yayin da Ankara ke jaddada kudurinta na kare sararin samaniyarta tare da kira ga zaman lafiya.

Newstimehub

Newstimehub

5 Mar, 2026

823fab7e5b51f78d55cd43338dc75e5bc95cfa48fd4da2f5e7330c6229b470a9

Ma’aikatar Tsaron Turkiyya ta ce rundunonin tsaron sama na NATO sun dakile wani makami mai linzami da aka harba daga Iran a yankin Gabashin Bahar Rum.

Daga baya an gano gutsuttsuren da suka fadi a lardin Hatay a kudancin Turkiyya, kuma an tabbatar cewa tarkacen garkuwar makamai ne da aka yi amfani da shi wajen kakkabo makamin. Hukumomi sun ce babu wanda ya rasa ransa a lamarin.

Mai magana da yawun ma’aikatar, Rear Admiral Zeki Akturk, ya ce Turkiyya ta kuduri aniyar kare ‘yan ƙasarta da kuma sararin samaniyarta. Ya kara da cewa Ankara na aiki tare da NATO da sauran abokan hulɗa domin mayar da martani ga duk wani barazana daga kowace hanya.

Akturk ya bayyana cewa Turkiyya na sa ido sosai kan rikicin da ya kunno kai tsakanin Iran, Amurka da Isra’ila, amma ya jaddada cewa ƙasar na fifita zaman lafiya. Ya ce Ankara na shirye ta bayar da gudunmawa wajen warware rikicin ta hanyar diflomasiyya, yana mai cewa matsalolin yankin za a iya magance su ne ta hanyar tattaunawa.

Ya kuma tabbatar da cewa duk da rikicin da ke faruwa a yankin, babu wani abin da ba a saba gani ba a kan iyakar Turkiyya da Iran, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da sa ido tare da ƙarfafa matakan tsaro.

Majiyar Labari: TRT HAUSA