‘Yan majalisar dokokin Amurka da ke wakiltar biranen da za su karɓi baƙuncin Gasar Kofin Duniya ta FIFA sun bayyana damuwa kan jinkirin shirye-shiryen tsaro, suna gargadin cewa matsalolin na iya zama babbar barazana yayin da gasar ke ƙaratowa. A zaman sauraron ra’ayin jama’a na Kwamitin Tsaron Cikin Gida, shaidu sun danganta jinkirin da dakatar da wasu kuɗaɗen FEMA da kuma rashin cikakken haɗin-kai tsakanin hukumomin yankuna da gwamnatin tarayya.
Dakatar da ayyukan FEMA zuwa ma’aunin gaggawa ya shafi kuɗaɗen tallafi da aka ware wa biranen masauki, ciki har da daruruwan miliyoyin daloli da aka tanada don manyan ayyukan tsaro. Jami’ai daga birane kamar Miami da Foxboro sun ce rashin samun kuɗaɗen da ake bukata na iya jawo soke wasu shirye-shirye, musamman Fan Fest da kuma wasu wasanni.
Masana tsaro sun ce lokaci na ƙurewa, suna mai jaddada muhimmancin ƙarfafa tsare-tsaren kariya, musamman kan barazanar jiragen sama marasa matuƙi da sauran barazanar tsaro. Wasu sassan ‘yan sanda, ciki har da Kansas City, sun ce ba su da isassun ma’aikata don rufe dukkan buƙatun tsaro.
Gasar Kofin Duniya, wadda Amurka, Mexico da Canada ke ɗaukar baƙunci, za ta fara ne a watan Yuni. Jimillar birane 11 a Amurka ne za su karɓi baƙuncin wasannin, yayin da jami’ai ke kira ga gaggauta sakin kuɗaɗen tsaro domin kauce wa matsaloli.














