A kalla makamai masu linzami goma ne jiragen yakin Amurka da Isra’ila suka harba a safiyar Talata kan wasu yankuna na Pardis da Damavand a Tehran, babban birnin Iran. Haka kuma an ji karar fashewar abubuwa a birnin Isfahan, duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance da ta fayyace takamaiman wuraren da aka kai hare-haren.
Rahotanni sun ce jiragen yakin sun kai farmaki ne da safe, lamarin da ya sake tayar da hankula a kasar. Kafofin yada labarai na cikin gida sun tabbatar da jin karar fashewa a Isfahan, amma har zuwa yanzu hukumomi ba su bayyana cikakken bayani kan illar da harin ya yi ba.
Wannan sabon farmaki na zuwa ne bayan Amurka da Isra’ila sun fara kai hare-hare kan Iran tun ranar 28 ga Fabrairu, duk da cewa a wancan lokaci ana tattaunawa tsakanin Tehran da Washington. Iran ta mayar da martani da kai hare-hare kan wasu wurare a Isra’ila da kuma kasashen yankin da ke dauke da sansanonin sojin Amurka.
Rahotanni sun kuma ce hare-haren sun yi sanadin mutuwar Jagoran Koli na Iran, Ali Khamenei, tare da wasu manyan jami’ai. Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran ta sanar da cewa hare-haren sun jawo mutuwar mutane 555 da jikkata 747.














