Gwamnatin Iraq ta sanar da rage yawan danyen man fetur da take hakowa bayan raguwar fitar da mai sakamakon rufe mashigar Strait of Hormuz da Iran ta yi. Ma’aikatar man fetur ta Iraq ta ce wannan mataki ya biyo bayan tashin hankali a yankin, amma rage hakar man ba zai shafi aikin matatun mai ko samar da kayayyakin man fetur domin biyan bukatar cikin gida ba.
Ma’aikatar ta kara da cewa matatun mai a kudanci da tsakiyar kasar da kuma arewa na ci gaba da aiki ba tare da tangarda ba, domin tabbatar da wadatar man fetur ga jama’a. Haka kuma an sanar da dakatar da hakar mai a filin mai na Rumaila da ke Basra bayan rufe mashigar Hormuz.
Rufe wannan mashiga ya jawo damuwa a kasuwannin duniya saboda kusan kashi daya cikin hudu na cinikin man fetur na duniya na wucewa ta nan. Masana sun yi gargadin cewa rikicin Gabas ta Tsakiya na iya haifar da tashin farashin makamashi da kuma matsin tattalin arziki a duniya.














