Gwamnatin Türkiye ta kira jakadan Iran, Mohammad Hassan Habibollahzadeh, zuwa Ma’aikatar Harkokin Waje domin nuna damuwa kan wani makami mai linzami da aka harba daga Iran wanda ya nufi sararin samaniyar Turkiyya. Hukumomin Ankara sun bayyana cewa wannan lamari ya sa suka gabatar da korafi a hukumance ga jakadan.
Haka kuma Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya tattauna da takwaransa na Iran Abbas Araghchi ta waya, inda ya bukaci a guji duk wani mataki da zai kara tsananta rikicin yankin.
A baya dai Ma’aikatar Tsaron Turkiyya ta bayyana cewa na’urorin kariyar makamai masu linzami na NATO sun gano tare da dakile makamin kafin ya shiga sararin samaniyar Turkiyya bayan ya ratsa yankunan Iraq da Syria. Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke kara tsananta.














