Turkiyya

Türkiyya Ta Soki Hare-Haren Amurka da Isra’ila Kan Iran

Türkiyya ta yi Allah-wadai da hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran, tana gargadin cewa rikicin na iya rikidewa zuwa babbar barazana ga daukacin yankin.

Newstimehub

Newstimehub

2 Mar, 2026

a2ccce371d21d8610c6bb98a13e4e33906254d5a64555bb4e6fc9c43f6fb3561

Gwamnatin Türkiyya ta bayyana hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a matsayin “hari na zalunci kuma ba bisa ka’ida ba,” tana mai cewa ba su da wani halacci a karkashin dokokin kasa da kasa.

Kakakin jam’iyyar AK, Ömer Çelik, ya ce kai hari a lokacin da ake kokarin warware rikici ta hanyar diflomasiyya na iya haifar da mummunan sakamako, yana mai jaddada cewa bai kamata a rika amfani da tattaunawa a matsayin rufa-rufa domin kai hari ba.

Çelik ya mika ta’aziyya ga al’ummar Iran kan asarar rayukan fararen hula da manyan shugabanni, tare da kira da a gaggauta komawa teburin sulhu. Ya kuma yi gargadin cewa yunkurin sauya gwamnati ko kai hari kan shugabancin kasa mamba a Majalisar Dinkin Duniya na iya haddasa rikici mai zurfi da kuma yaki mai tsawo a yankin.

A lokaci guda, ya gargadi Iran da kada ta fadada rikicin ta hanyar kai hari kan wasu kasashe, yana mai cewa dole ne a bambance tsakanin kare kai da kuma matakan da za su iya jefa yankin cikin mummunan yaki. Ya bayyana cewa Ankara na sa ido sosai tare da daukar matakan kariya, musamman kan batun ‘yan gudun hijira, tattalin arziki, tsaron kasa da kuma kare ‘yan kasar Turkiyya a kasashen waje.

Hukumomin Turkiyya sun ce ofisoshin jakadanci na aiki ba dare ba rana domin taimaka wa ‘yan kasarsu da rikicin ya shafa. Hare-haren dai sun fara ne bayan Amurka da Isra’ila sun kai farmaki kan Iran, lamarin da ya jawo martanin Tehran ta hanyar hare-haren jiragen yaki marasa matuki da makamai masu linzami kan Isra’ila da wasu wurare a yankin.

Majiyar Labari: TRT HAUSA