Gwamnatin Turkiyya ta gano wasu kayayyakin tarihi guda 76 da aka yi amannar mallakin Nijeriya ne, lamarin da ke ƙara haskaka ƙoƙarin dawo da kayan al’adu da aka kwashe daga Afirka tare da ƙarfafa dangantakar al’adu tsakanin ƙasashen biyu.
Jakadan Turkiyya a Nijeriya, Mehmet Poroy, ya bayyana hakan a Abuja yayin wata ziyara da ya kai wa Ministar Al’adu, Yawon Buɗe Ido da Tattalin Arzikin Kirkire-kirkire, Hannatu Musa Musawa. Ya ce kayayyakin sun ƙunshi abubuwan katako da ƙarafa da aka gano tun a watan Mayun da ya gabata, kuma ana kyautata zaton asalinsu daga Nijeriya ne.
Poroy ya ce Turkiyya na fatan kulla yarjejeniyar haɗin gwiwa da Nijeriya kan mayar da waɗannan kayan tarihi gida, a lokacin ziyarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kai Turkiyya. Ya jaddada cewa wannan mataki zai taimaka wajen bunƙasa fahimtar al’adu, tare da kafa cibiyar al’adu a Nijeriya domin tallafa wa fasahar gargajiya da ilimantar da matasa.
Minista Hannatu Musawa ta maraba da shirin, tana mai cewa dawo da kayan tarihi na da matuƙar muhimmanci ga kare gadon al’adun Nijeriya. Ta kuma nuna sha’awar ƙarfafa haɗin gwiwa da Turkiyya a fannoni kamar masana’antar fina-finai, musayar al’adu, da bunƙasa rawar mata a harkokin fasaha da ado.














