Fiye da mutane 100 sun mutu sakamakon wata mummunar zaftarewar ƙasa da ta afku a wani wurin hakar ma’adinin coltan a gabashin Democratic Republic of the Congo. Lamarin ya faru ne a yankin Rubaya na lardin North Kivu bayan ruwan sama mai ƙarfi ya raunana ƙasar da ake hakar ma’adinan.
Rahotanni sun ce yawancin wadanda suka mutu ma’aikatan hakar ma’adinai ne na gargajiya da kuma ‘yan kasuwa da ke dogaro da aikin hakar ma’adinai domin samun abin yi. Kungiyoyin ceto na ci gaba da tono kasa domin nemo wadanda suka makale, duk da cewa aikin yana da wahala saboda rashin kayan aiki da kuma kasa mai laushi.
Yankin Rubaya dai na karkashin ikon kungiyar ‘yan tawaye ta M23 tun shekarar 2024, kuma an san shi da samar da ma’adinai masu muhimmanci wajen kera kayan lantarki a duniya. Lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da rikice-rikice ke ci gaba da tsananta a yankin North Kivu.














