Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) sun kama wani tsohon kansila da ya yi wa’adin mulki biyu a Jihar Legas tare da kama wasu miyagun ƙwayoyi a jihohi daban-daban na ƙasar, a wani ɓangare na ƙara kaimi da suke yi wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi a fadin Nijeriya.
Wanda ake zargin mai suna Sheleru Sadiq Olalekan, mai shekaru 45, tsohon kansila ne a Ƙaramar Hukumar Ibeju-Lekki ta Jihar Legas kuma a halin yanzu mataimaki ne na musamman ga wani ɗan majalisa. An kama shi ne a gidansa da ke Ilado a Ibeju-Lekki na Jihar Lagos.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi ya bayyana cewa jami’an hukumar sun kai samame gidansa ne bayan samun sahihan bayanan sirri, inda suka gano kilogiram 40 na tabar wiwi nau’in skunk, a ɗaya daga cikin ɗakunan gidan.
A yayin tambayoyi, Olalekan ya bayyana wa hukumar cewa miyagun ƙwayoyin da aka samu nasa ne, haka kuma gidan da aka same su a ciki nasa ne, kamar yadda NDLEA ɗin ta bayyana.
Ya kuma tabbatar da cewa a baya ya yi wa’adin mulki biyu inda ya wakilci al’ummar Orimedu a matsayin kansila.
A wani samame daban na daban a Abuja, jami’an NDLEA sun kama wani ɗan kasuwa mai shekaru 32 mai suna Emeka Hyginus Okwor, wanda ke tafiya a mota daga Obollo-Afor a Jihar Enugu zuwa Zuba a Babban Birnin Tarayya.
A binciken da aka yi a cikin kayansa an gano ƙwayoyi 1,000 na tapentadol da aka ɓoye a cikin ƙunzugun jarirai.
Rahotanni sun ce wanda ake zargin ya amsa cewa yana kai waɗannan kwayoyi ne zuwa ƙauyen Guduwa da ke ƙaramar hukumar Gurara ta Jihar Neja, inda yake gudanar da wani shagon sayar da kayan abinci.














