Aƙalla mutane 42 ne suka rasa rayukansu a Kenya bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka yi na kwanaki da dama ya haddasa ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na ƙasar. Mafi muni ya faru ne a babban birnin ƙasar, Nairobi, inda mutane 26 suka mutu bayan ruwa ya mamaye ƙananan unguwanni da matsugunan marasa ƙarfi, ya nutse gidaje tare da kwashe motoci yayin da koguna suka cika suka malala.
Rahotanni daga ‘yan sanda sun ce an kuma samu karin mace-mace a wasu gundumomi yayin da ruwan sama ya mamaye hanyoyi, ya dakatar da zirga-zirga, tare da kawo cikas ga rayuwar yau da kullum a garuruwa da dama. A halin yanzu jami’an ceto na ci gaba da aikin bincike da ceto a yankunan da abin ya fi shafa.
Ministan Ma’aikatan Jama’a da Shirye-shiryen Musamman na Kenya, Geoffrey Ruku, ya tabbatar da adadin wadanda suka mutu, yana mai cewa gwamnati ta tura tawagogin agaji domin taimaka wa al’ummomin da bala’in ya shafa. Ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta dauki nauyin kudin jinyar wadanda suka jikkata tare da kudin jana’izar iyalan wadanda suka rasa rayukansu. A lokaci guda, ambaliyar ruwan ta lalata gidaje, shaguna da wasu muhimman gine-gine, yayin da ake ci gaba da kwashe mutane daga yankunan da ruwa ya mamaye.














