Afirka

Sojojin Sudan Sun Ce Sun Daƙile Harin RSF a El Tina

Sojojin Sudan sun ce sun fatattaki RSF daga El Tina, duk da ikirarin RSF na kwace iko da birnin.

Newstimehub

Newstimehub

22 Feb, 2026

1770808251750 kzrwa e4a45436890c2b0162c9fb2a54d191f2aafa0f9bef248ec7dc766af75be9b6d2

Sojojin Sudan tare da haɗaƙar ƙawayensu sun daƙile wani hari da rundunar Rapid Support Forces (RSF) ta kai a birnin El Tina da ke kan iyaka da Chad. Ƙungiyar farar hula ta Resistance Committees a Al Fasher ta ce dakarun RSF sun kutsa birnin a ranar Asabar, amma suka ja da baya bayan arangama.

Gwamnan Darfur, Minni Arko Minawi, ya zargi RSF da kai hari kan fararen hula, yana mai wallafa bidiyoyi da ke nuna yadda aka ƙwace motocin yaƙi da makamai. A gefe guda, RSF ta yi iƙirarin ta kwace iko da El Tina a wata sanarwa da ta fitar.

RSF na riƙe da yawancin jihohin Darfur guda biyar, yayin da sojojin ƙasa ke iko da mafi yawan sauran yankunan ƙasar, ciki har da Khartoum. Rikicin da ya fara a Afrilun 2023 ya haddasa babbar matsalar jin kai, inda dubban mutane suka mutu, miliyoyi suka rasa matsuguni, tare da barazanar yunwa.

Rahotanni na nuni da cewa Darfur na daga cikin wuraren da suka fi fuskantar tasirin yaƙin, yayin da al’umma ke fama da rashin tsaro da karancin abinci.

Majiyar Labari: TRT HAUSA