Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya tattauna ta waya da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, kan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran. A yayin tattaunawar, Araghchi ya ce hare-haren sun shafi makarantu, asibitoci, gidajen jama’a da wuraren tarihi, yana mai cewa hakan babban take ne ga dokokin kasa da kasa.
Araghchi ya kuma jaddada cewa al’ummar duniya da kungiyoyin kasa da kasa na da alhakin yin Allah-wadai da irin wadannan hare-hare. Ya kara da cewa Iran ta sha gargadin cewa za ta mayar da martani idan aka kai mata hari daga sansanonin sojin Amurka da ke kasashen yankin.
A nasa bangaren, Antonio Guterres ya yi kira da a guji kara tsananta rikici a yankin. Ya jaddada muhimmancin daukar matakan da za su hana rikicin yaduwa zuwa wasu kasashe a Gabas ta Tsakiya.














