A wani hukunci da ya ja hankalin jama’a a jihar Taraba, babbar kotun majistire ta ɗaya da ke Jalingo ta yanke wa mutum uku hukuncin ɗaurin shekara 10 a gidan yari ba tare da zaɓin tara ba bayan an same su da laifin safarar makamai.
Rahotanni sun nuna cewa Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya (DSS) ce ta gurfanar da mutanen uku – Sakina Garba, Ali Gono da Ibrahim Abdulrashid – a gaban kotu bayan kama su tsakanin watan Janairu da Fabrairun shekarar 2026.
Gidan talabijin na gwamnatin Nijeriya (NTA) ya ruwaito cewa kama mutanen ya biyo bayan bayanan sirri da jami’an tsaro suka samu game da shirin safarar makamai daga ƙauyen Bantaje da ke ƙaramar hukumar Wukari a jihar Taraba domin kai su ga wani fitaccen mai garkuwa da mutane.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an kama su ne a kan hanyar Wukari zuwa Jalingo, inda suka ɓoye makaman cikin buhunan abinci domin kauce wa zargin jami’an tsaro.
A cewar majiyar da NTA ya ambato, an samu bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, harsasai 984 masu tsawon 7.6mm, da kuma harsasai 105 masu tsawon 7.82mm. Haka kuma an gano gidan harsasan AK-47 guda 14 tare da na’urorin POS guda uku da kuma kuɗi naira 200,200 a cikin buhunan.
A wani lamari makamancin haka kuma, wata mata mai suna Halima Haliru Umar ta amsa laifin safarar makamai a gaban babbar kotun Tarayya da ke Abuja bayan jami’an DSS sun gabatar da harsasai 302 da aka samu a hannunta.
Bayan amincewarta da laifin, alƙalin kotun, Mai Shari’a Haywa Joseph Yilwatda, ya ɗaga zaman kotun zuwa ranar 8 ga watan Mayu domin yanke mata hukunci.
Tun da farko, shaidan DSS ya bayyana wa kotu cewa an kama Halima Umar a jihar Filato yayin da take ɗauke da harsasai 302, wanda ake zargin tana kan hanyarta ta kai su ga wani sanannen mai garkuwa da mutane.
Shaidan ya kuma gabatar da harsasan da aka kwace, rahoton bincike, da kuma kuɗaɗen da aka samu daga hannunta a matsayin hujjoji a gaban kotu.














