Wasu da ake zargin ’yanta’addan Boko Haram ne sun ƙone makarantun firamare da sakandare da ke ƙauyen Kautikari a Ƙaramar Hukumar Chibok ta Jihar Borno.
Lamarin na zuwa ne bayan an sace ɗaliban makarantar Firamare da Sakandare ta Mussa da ke Askira-Uba kusan wata guda da ya gabata, ba tare da an gano inda suke ba.
Majiyoyin tsaro sun ce maharan sun kai farmaki garin da misalin ƙarfe 7 na yammacin ranar Asabar. Garin dai ya sha fama da hare-hare a lokuta da dama a baya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
“Ya zuwa yanzu ba a samu asarar rai ba, amma mazauna yankin sun tsere zuwa cikin daji domin neman tsira,” in ji ɗaya daga cikin majiyoyin.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa ’yanta’addan sun kai hari ƙauyen watanni da suka gabata, amma ba su lalata wata kadarar gwamnati ko ta masu zaman kansu ba.
“Abin mamaki ne yadda suka ƙone makarantar firamare da makarantar sakandaren jeka-ka-dawo. Irin wannan hari ba kasafai ake ganin sa ba,” in ji shi.
Duk ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sanda, ASP Nahum Kenneth Daso, bai yi nasara ba, domin wayarsa ba ta shiga, a cewar jaridar.

















