Kasashen Turai da suka hada da Birtaniya, Faransa, Jamus, Italiya, Netherlands tare da Japan sun bayyana shirinsu na taimakawa wajen tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, bayan hare-haren da ake dangantawa da Iran a yankin Gulf. A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, shugabannin sun ce suna da niyyar bayar da gudummawa domin tabbatar da wucewar jiragen kasuwanci cikin aminci.
Sun kuma yi kakkausar suka ga hare-haren da aka kai kan jiragen ruwa marasa dauke da makamai da kuma ababen more rayuwa, ciki har da cibiyoyin mai da iskar gas. Sun bukaci Iran da ta dakatar da duk wani mataki na tashin hankali, ciki har da amfani da makamai masu linzami, jiragen yaki marasa matuki da kuma duk wani yunkuri na rufe mashigar ga kasuwanci.
Kasashen sun jaddada cewa ‘yancin zirga-zirgar ruwa muhimmin ginshiki ne na dokokin kasa da kasa, kuma duk wani katsalandan a harkar jiragen ruwa barazana ce ga zaman lafiya da tsaron duniya. Sun kuma yi kira da a dakatar da kai hare-hare kan ababen more rayuwa na fararen hula, musamman a bangaren makamashi.
Dangane da makamashi, sun maraba da matakin da Hukumar Makamashi ta Duniya ta dauka na sakin ajiyar mai domin rage tasirin rikicin, tare da alkawarin daukar karin matakai don daidaita kasuwa. Wannan na zuwa ne yayin da rikici ke kara tsananta tun bayan hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran, wanda ya haddasa tashin farashin mai a kasuwannin duniya.
Farashin danyen mai na Brent ya tashi zuwa dala 113.55 kan ganga, yana nuna yadda rikicin yankin ke tasiri kai tsaye ga tattalin arzikin duniya.














