Ministan harkokin cikin gida na Nijeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa sama da mutane 840,000 daga ƙasashe daban-daban suna nan a ƙasar bayan wa’adin bizar su ya ƙare. Ya ce wannan lamari ya zama babban ƙalubale a fannin kula da hijira, kuma an gano wannan adadi ne ta hanyar sabon tsarin sa ido da gwamnatin ta inganta kwanan nan.
A cewarsa, warware matsalar masu wuce wa’adin biza zai taimaka wajen rage wasu manyan laifuka da suka haɗa da safarar mutane da fasa-kaurin baki. Ya ƙara da cewa hijira ba bisa ka’ida ba matsala ce ta duniya, don haka tana buƙatar haɗin kai tsakanin ƙasashe, musamman ta hanyar yarjejeniyoyi da ke ba da damar mayar da mutanen da ba su da hurumin ci gaba da zama cikin mutunci.
Ministan ya kuma yi magana kan yarjejeniyar hijira da aka sanya wa hannu tsakanin Nijeriya da Birtaniya, inda ya jaddada cewa yarjejeniyar ta shafi ‘yan Nijeriya ne kawai kuma ta ginu ne bisa tsarin musayar fahimta tsakanin ƙasashen biyu. Ya musanta rahotannin da ke cewa za a turo fursunonin ƙasashen waje zuwa Nijeriya, yana cewa gwamnatin nan ba za ta taɓa amincewa da irin wannan tsari ba.
Har ila yau, ya ce gwamnati ta bayyana komai a fili game da yarjejeniyar, kuma ba ta da alaƙa da shirin Rwanda da ya jawo ce-ce-ku-ce a baya. Ya tabbatar da cewa duk wani ɗan Nijeriya da za a dawo da shi ƙarƙashin wannan tsari za a yi masa mu’amala cikin mutunci tare da kare masa haƙƙoƙinsa na asali, yana mai cewa babu ɗan Nijeriya da zai yi asara daga wannan yarjejeniya.
Majiyar Labari: Channels News













