Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya roƙi shugabancin Majalisar Dattawa ta 10 da ta yi gyaran kundin tsarin mulki domin samar da gindin doka na kafa ‘yan sandan jihohi. Ya bayyana hakan ne yayin wani karin kumallo na addinai daban-daban da sanatoci a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Tinubu ya ce batun kafa ‘yan sandan jihohi ya zama gaggawa, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro a matakin al’umma da bai wa jihohi damar mayar da martani cikin sauri ga barazanar tsaro. Ya jaddada cewa tsarin ‘yan sanda mai rarraba iko zai cike gibin tsarin tsaron tarayya tare da ƙarfafa aikin leƙen asiri da tsaron al’umma.
Shugaban ya yabawa haɗin kan da ke tsakanin bangaren zartarwa da Majalisar Dattawa, yana mai cewa haɗin kai ne zai taimaka wajen yaƙi da ta’addanci da ‘yan bindiga. Haka kuma ya gode wa Majalisar kan goyon bayan da ta ba gwamnatinsa a sauye-sauyen tattalin arziki, ciki har da cire tallafin man fetur da manufofin haraji.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yabawa Shugaba Tinubu, yana mai cewa sauye-sauyen da aka aiwatar sun ƙara kuɗaɗen shiga ga jihohi. Ya kuma yi addu’a ga nasarar gwamnatin.














