Gwamnatin Birtaniya ta bayyana cewa tana ƙara ƙaimi domin kare gidaje daga matsin tattalin arziki da ke da alaƙa da rikicin Gabas ta Tsakiya, musamman a yankin Strait of Hormuz wanda ke da muhimmanci wajen jigilar mai da gas a duniya. Jami’ai sun ce suna daukar matakai tun da wuri don rage illar da hakan ka iya haifarwa ga rayuwar jama’a.
A cewar jami’in baitul-mali, Darren Jones, gwamnati na shirin fuskantar duk wata tangarda da ka iya jawo hauhawar farashi. Duk da cewa a halin yanzu babu ƙarancin mai, ana gudanar da taruka akai-akai don tabbatar da daidaiton hanyoyin samar da kayayyaki da kuma kauce wa sayayya cikin firgici.
Sai dai an gargadi jama’a cewa za su iya fuskantar karin kuɗin lantarki, abinci da kuma tafiye-tafiye nan gaba. Wadannan ƙarin farashin na da alaƙa da hauhawar farashin makamashi a duniya da kuma tangardar sufuri da rikicin ya haifar.
Jones ya ƙara da cewa ko bayan rikicin ya lafa, tasirin tattalin arzikin na iya ɗaukar watanni takwas ko fiye, wanda ke nufin gidaje za su ci gaba da jin nauyi na wani lokaci. A nasa bangaren, Firaminista Keir Starmer ana sa ran zai jagoranci matakan haɗin gwiwa da sauran ƙasashe domin daidaita kasuwanni da bude hanyoyin kasuwanci.
Hukumomi na kuma shirya matakan gaggawa idan abubuwa suka tsananta, ciki har da yiwuwar ƙarancin kayayyaki, tare da tanadin hanyoyin tallafi domin rage wa jama’a nauyi.
MAJIYAR LABARI: AA













