Nijeriya

‘Yanta’addan Lakurawa sun kashe jami’an hukumar kwastam biyu a Jihar Kebbi ta Nijeriya

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya yi Allah wadai da harin kuma ya ce hukumomin tsaro na aiki domin kama waɗanda suka yi aika-aikar.

Newstimehub

Newstimehub

14 May, 2026

7b5ae34ecf30462bce423c72af55a840ea432cfd9c4d3b133f17c2a65d31c903

Aƙalla jami’an kwastam biyu ne wasu da ake zargin ‘yanta’addan Lakurawa ne suka kashe a ƙauyen Tugar da ke ƙaramar hukumar Bagudu ta jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Nijeriya.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Laraba yayin da mayaƙan Lakurawa suka far ma jami’an a wani shingen bincikensu da ke garin.

Gidan talbijin na tarayyar Nijeriya NTA ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kazalika Jaridar Punch ta Nijeriya ta ambato wata majiya wadda ta ce ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su wani babban jami’i ne na hukumar kwastam wanda ‘yanta’addan suka ƙona a cikin ginin da yake barci a lokacin da suka kai harin.

Majiyar ta bayyana cewa lamarin ya auku ne da kimanin ƙarfe 3:00 na dare a ranar Laraba.

Majiyar ta ce, “‘Yanbindigar sun far ma wuraren bincike biyu ne da ke kusa da juna sosai.

“Sun harbe wani ƙaramin jami’in hukumar yayin da suka ƙone wani babban jami’i da ransa.

“Sun zo ne a cikin wata babbar mota inda suka yi shigar masu dakon dabbobi, lamarin da ya shammaci jami’an.

“Sauran jami’an biyu da suka ji raunuka na harbin bindiga a halin yanzu suna karɓar magani a asibiti,” in ji majiyar.

Sai dai kuma da aka tuntuɓe shi, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar hukumar kwastam ta jihar Kebbi, Mustapha Mubarak, ya ce rundunar za ta fitar da wata sanarwa bayan ta samu cikakken bayani game da lamarin.

Bai musanta ko kuma tabbatar aukuwar lamarin ba, yana mai cewa, “Za mu fitar da wata sanarwa da zarar mun samu cikakken rahoto.”

Sai dai kuma mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya yi Allah wadai da harin kuma ya ce hukumomin tsaro na aiki domin kama waɗanda suka aikata aika-aikar.