Nijeriya

Tinubu ya yi gargaɗi kan siyasar ‘a-mutu-ko-a-yi-rai’ a zaɓukan fid da gwani na Jam’iyyar APC

“Zaɓe muhimmin sinadirai ne na dimokraɗiyya. Idan an gaza cim ma matsaya a kan ɗan takara (concensus), na yi kira ga dukkanmu mu shiga zaɓukan fid da gwani a matsayin ‘yanuwa maza da mata,” in ji shugaban.

Newstimehub

Newstimehub

15 May, 2026

2026 03 28t085353z 718834402 rc29dkadjlv4 rtrmadp 3 nigeria politics

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi gargaɗi ga ‘yan jam’iyyar APC mai mulki ranar Alhamis kan faɗa a tsakaninsu da kuma siyarsar ‘a-mutu-ko-a-yi-rai’ yayin da jam’iyyar ke fara zaɓukan fid da gwaninta gabanin zaɓukan shekarar 2027.

A wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa game da fara zaɓukan fid da gwanin APC a faɗin ƙasar, Tinubu ya yi kira ga masu neman takara da shugabannin jam’iyya da kuma wakilai su gudanar da harkokinsu cikin lumana yayin da suke ɗabbaka ƙa’idojin dimokuraɗiyya a cikin jam’iyya da adalci da kuma yarda da duk yadda sakamakon zaɓukan za su kasance.

Shugaban ya bayyana zaɓukan fid da gwanin, da za a fara da na masu neman takarar majalisar wakilan tarayya kuma a ƙarƙare da na masu neman takarar shugaban ƙasa ranar 25 ga watan Mayu, a matsayin mai muhimmanci ga haɗin kai da kuma makomar jam’iyyar mai mulki.

“Kada mu yi salon siyasar baya; siyasar ‘a-mutu-ko-a-yi-rai’ wadda muka bari a bayanmu. Bai dace siyasa ta kasance harka ta nasarar wani ta kasance rashin wani ba,” in ji Tinubu.

Ya yi kira ga masu neman takara su fuskanci lamarin a matsayin wata dama ta ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar maimakon haddasa rarrabuwar kai.

“Zaɓe muhimmin sinadiri ne na dimokuraɗiyya. Idan an gaza cim ma matsaya a kan ɗan takara (concensus), na yi kira ga dukkanmu mu shiga zaɓukan fid da gwani a matsayin ‘yan’uwa maza da mata,” in ji shugaban.

“Dukkan masu shiga zaɓukan fid da gwanin, a matsayin masu neman takara ko masu zaɓe, dole su kiyaye zaman lafiya kuma su shirya domin amincewa da sakamakon zaɓen ba tare fa faɗa ba domin muradun jam’iyyar da na ƙasar baki ɗaya,” in ji shi.

Tinubu ya yi gargaɗi kan matakan da za su iya yin zagon ƙasa ga dimokuraɗiyya da kuma haɗin kan jam’iyya, yana mai jaddada cewa dole waɗanda suka yi nasara su ƙauce wa nuna murnar nasara da yawa kuma waɗanda suka sha kaye su amince da sakamakon cikin kyakkyawan yanayi.

“A cikin ko wace takara, za a sami wanda zai yi nasara da wanda zai sha kaye. Na yi kira ga ga waɗanda suka yi nasara kada su yi tsokana a cikin nasararsu kuma waɗanda suka sha kaye su nuna hali na dattaku ta hanyar karɓar sakamakon da kuma shiryawa domin nan gaba,” in ji shi.

Shugaban ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar APC a faɗin ƙasar su rungumi tsarin cim ma matsaya a kan ‘yan takara (concensus) idan hakan zai yiwu, yana mai cewa wannan zaɓin zai iya rage tashe-tashen hankula tsakanin ‘yan jam’iyyar.

“Na sani cewa , bisa tanade-tanaden dokar zaɓen ta shekarar 2026 da kuma tsarin mulkin jam’iyyarmu, shugabanni a matakai da dama sun fara tattaunawa domin cim ma matsaya a kan ‘yan takara (concensus).

“Wani zaɓi ne da za a iya yaba wa wanda zai taimaka wajen rage ce-ce-ku-ce da ƙiyayya tsakanin ‘ya’yan jam’iyya,” kamar yadda ya ƙara bayyanawa.

Tinubu ya kuma yi kira ga shugabannin jam’iyya da gwamnoni su tabbatar da adalci ta hanyar samar da yanayi na takara na bai-ɗaya ga dukkan masu neman takara.

“Ga shugabannin jam’iyya da gwamnoninmu da sauran shugabanni, na yi kira a gare ku ku yi adalci. Dole ku fi ƙarfin son zuciya domin bai wa dukkan masu neman takara yanayi na bai-ɗaya,” in ji shi .

Shugaban ya kuma yi kira da a saka ƙarin mata da matasa cikin harkar siyasar jam’iyyar.

“Saka mata da matasa abu ne da zuciyata ke ƙauna. Na yi kira ga masu zaɓe a zaɓukan fid da gwani da kuma shugabanni a dukkan matakai su yi tunani na musamman game da matanmu da matasa a zaɓen,” in ji shi .

Kazalika Tinubu ya gargaɗi ‘yansanda da sauran jami’an tsaro game da yin katsalandan a cikin zaɓukan fid da gwani sannan su tabbatar da doka da oda.