Amurka ta ƙaddamar da gagarumin hararin bama-bamai ta sama a kan Iran, kwana guda bayan da aka harbo wani jirgi mai saukar ungulu na yaƙi na Amurka kusa da Mashigar Hormuz.
Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya bayyana cewa an ji sautin bama-bamai da jiniyar tsarin tsaron sararin samaniya a garuruwa da dama da ke gaɓar tekun Iran, ciki har da birnin Sirik da kuma tsibirin Qeshm.
Cibiyar ayyukan sojin ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata cewa, “hare-haren kare kai” sun fara ne da misalin karfe 5 na yamma agogon Washington, bisa umarnin Trump.
“Wannan aiki ne na mayar da martani da ya dace kan tsokanar da Iran ta yi ba tare da wani dalili ba,” in ji rundunar a cikin wata sanarwa.
Kamfanin dillancin labarai na Mehr na Iran, wanda ya ambato mazauna yankin, ya bayar da rahoton fashewar manyan bama-bamai a yankin Sirik.
Kafofin watsa labarai na gwamnatin Iran sun ruwaito cewa an kuma kai hari a tsibirin Qeshm da kuma tashar jiragen ruwa ta Bandar Abbas.
Trump ya sha alwashin mayar da martani
“Ina jin yana da matuƙar muhimmanci a mayar da martani. Sun harbo helikwafta, mu kuma muna mayar da martani a daidai lokacin da muke magana,” Trump ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta ABC News game da hare-haren na ramuwar gayya da Amurka ke kai wa Iran.
“Wannan martani ne ga abin da suka yi… ga helikwafanmu a daren jiya, kuma na yi amanna cewa martanin ya kamata ya kasance mai ƙarfi sosai, mai cike da nuna iko, kuma abin da wannan harin yake yi kenan,” in ji shugaban na Amurka.
A gefe guda kuma, shafin yanar gizo na kafar labaran Axios, ya ambato wani babban jami’in Amurka, yana cewa dakarun sojin Amurka sun kai hari kan wasu batirorin kariyar sararin samaniya da na’urorin kula da jirage na Iran a kewayen Mashigar Tekun Hormuz.
Axios ya ce zagaye na biyu na hare-haren a Iran yana gudana “yanzu haka” wanda ke nufar tsarin tsaron sararin samaniya da na’urorin kula da jirage.

















