Canada ta yi nasarar kafa tarihi zuwa matakin ‘yan-16 a gasar Kofin Duniya, bayan da ta doke Afirka ta Kudu da ci 1-0 a wasan farko na zagayen sili-ɗaya-ƙwale na gasar.
Ɗanwasan Canada, Stephen Eustaquio ne ya zura ƙwallo a ragar Afirka ta Kudu, kuma ƙwallon ce ta bai wa Canada nasarar zama ƙasa ta farko da ta tsallaka zagaye na gaba a gasar.
Wannan ne karon farko da duka ƙasashen biyu suka taɓa kai wa matakin sili-ɗaya-ƙwale a tarihin gasar, wanda ya sanya wasan ya yi tsauri.
A ƙarshe sai da wasan ya shiga ƙarin lokaci bayan kammala mintuna 90, kafin ɗanwasan Canada, Eustaquio ya karya lagon Afirka ta Kudu da bugun daga wajen da’irar raga.
Canada na buga wasanninta a birnin Los Angeles na Amurka, duk da tana cikin masu masauki tare da Amurka da Mexico.
Ta zo ta biyu a Rukunin B, kuma a yanzu za ta fafata da Netherlands ko kuma Morocco a birnin Houston a wasan zagayen ‘yan-16 wanda za a yi ranar 4 ga Yuli.

















